An Garƙame Hotel Saboda Damun Jama’a Da Hayaniya
Jami’an hukumar kare muhalli na jihar Lagos (LASEPA), sun rufe wurare da dama a jihar, bisa damun al’umma da ƙara da surutu.
LASEPA, ta bayyana hakan ne, ta cikin wani jawabi da ta wallafa a shafinta na X, da yammacin ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba.
Inda jawabin ke cewa, “LASEPA ta ɗauki matakan kawo ƙarshen damun Jama’a da ake yi da ƙara da surutai, jnda ta fara ta kan masu shiga haƙƙin jama’ar a ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba.
“Mun rufe wurare da dama a Lekki Phase I, Victoria Island, da Ajah.
“Wuraren sun haɗarda, Short Let Nigeria; Quays; da Lakers a Lekki Phase I. Rush Club da Lounge a Victoria Island.
“Bells Lounge; Bukky’s Sport; Fire & Ice Bar; Grand Play Hotel; da wurin cin abinci na Somewhere Restaurant & Bar, da ke Ajah.”.
Jawabin, ya kuma ƙara da bayyana cewar, an ɗauki wannan mataki ne, bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga al’umma kan damunsu da surutai da ƙararraki, waɗanda ke cutar da mazauna yankunan da wuraren su ke.