An Garƙame Masallaci A Lagos, Bisa Zargin Damun Mutane Da Ƙara
A ranar Litinin ne, Jami’an hukumar kiyaye muhalli ta jihar Lagos (LASEPA), su ka gudanar da gangamin garƙame wani Masallaci, tare da Cocinan da ke yankin Oshodi/Isolo, na jihar ta Lagos, bisa zargin damun mutane da ƙara.
LASEPA, ta bayyana ɗaukar wannan mataki ne, ta cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa ta X, a ranar Talata.
Inda rubutun ke cewa, “A cigaba da ƙoƙarin da ta ke yi na magance matsalar yawaitar hayaniya a muhalli, a jiya, LASEPA ta garƙame wasu muhimman wurare, da su ka haɗarda Masallaci, Kamfani, da Hotels, da ke yankin Oshodi/Isolo, bisa zargin shiga haƙƙin jama’ar da ke rayuwa a yankin”.
Jerin sunayen wuraren da lamarin ya shafa su ne: Masallacin Adura Agba Ratibi; Stag Engineering Nigeria Limited; Green Point Hotel; 4 Season Hotel and Suites; Big Apple Hotel and Suites; Honey Dew Hotel and Suites; Humble Signature Hotel and Suites; da New Ground Hotel.