Kotu

An Gurfanar Da Wata Mata A Gaban Kuliya, Bisa Zargin Satar Kuɗaɗen Abokiyar Zamanta

Wata mata mai suna, Hannah Bassey, ta gurfana a gaban babbar kotun Ƙaru, da ke Abuja, a ranar Laraba, bisa zarginta da satar zunzurutun kuɗi har Naira 200,000 mallakin Abokiyar zamanta da su ke ɗaki guda.

Ƴan Sanda na tuhumar Bassey, mai shekaru 48, wacce kuma ke zaune a Nyanya, ta Abuja ne, da laifukan karya ƙofar gida, tare da runtuma sata.

Sai dai wacce ake zargin, ta musanta aikata laifukan da ake zarginta da su.

Mai gabatar da ƙara, Mr. Ade Adeyanju, ya bayyanawa Kotun cewar, wacce ake zargin ta sace kuɗin wacce ke ƙararta ta ne da ya kai Naira 200,000. Inda ya ce kuma, ko a ya yin Jami’an ƴan sanda ke gudanar bincike kan lamarin, wacce ake zargin ta gaza bada gamsashshiyar amsar wurin da ta samu kuɗaɗen.

Mai gabatar da ƙarar ya kuma ce, laifukan sun saɓa da tanade-tanaden sashe na 354 da 288 na kundin Penal Code.

Alƙalin Kotun, Malam Yusuf Adamu, ya damƙa wacce ake zargin a hannun beli, kan kuɗi Naira 150,000, tare da wanda zai tsaya mata guda ɗaya, wanda shi ma zai ajiye makamancin wannan kuɗin.

Ya kuma ce, wajibi ne, a ajiye katin shaida, tare da bayanan Asusun wacce ake zargin ƙarƙashin kulawar Kotu.

Inda ya ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button