An Gurfanar Da Wata Mata A Kotu, Bisa Zargin Farmakar Jami’ar Ƴar Sanda
Rundunar ƴan sandan jihar Lagos, ta gurfanar da wata mata mai suna, Omorogbe Jennifer Soni a gaban Kotu, bayan da aka hangeta ta cikin wani faifan bidiyo, tana cin zarafin Jami’ar ƴar sanda, a yankin Ajah.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, shi ne ya bayyana hakan ranar Talata, 27 ga watan Fabrairun da mu ke bankwana da shi, ta shafinsa na X.
A cewar, Hundeyin dai, tuni aka garƙame Omorogbe ɗin a Cibiyar Gyaran Hali ta Kirikiri, kafin ranar da za a cigaba da sauraron Shari’ar, a watan Maris.
Ga abinda ya wallafa: “Rundunar ƴan sandan jihar Lagos, ta gurfanar da wata mata mai suna, Omorogbe Jennifer Soni ‘Mace’ mai shekaru 26 a gaban Kotu, bayan da wani faifan bidiyo ya nuna yadda ta ke cin zarafin wata Jami’ar ƴan sanda, a yankin Ajah, tun ranar 21 ga watan Fabrairun 2024.
“An gurfanar da Omorogbe a gaban Kotun ne kuma, washe garin ranar, 22 ga watan Fabrairu, a gaban Kotun Majistiri, da ke Ajah, kuma tuni aka aike da ita zuwa Cibiyar Gyaran Halin Mata ta Kirikiri, har zuwa ranar 27 ga watan Maris ɗin 2024, inda za a cigaba da sauraron shari’ar.
“Rundunar ƴan sandan jihar Lagos, na shawartar mazauna jihar da su kasance masu kiyaye doka da ƙa’ida a cikin ayyukansu na yau da kullum, domin kuwa dukkannin wanda aka samu da aikata laifi wajibi ne ya fuskanci hukunci”.