An Haifi Wata Jaririya Ɗauke Da Yatsu 26
An haifi wata jaririya a Asibitin Rajasthan, da ke Arewa Maso Yammacin ƙasar India, ɗauke da yatsun hannu guda 14, tare da na hannu kimanin 12.
Jaririyar dai, na ɗauke ne da yatsu bakwai-bakwai a kowanne daga cikin hannayenta, ya yin da ta ke da guda shida-shida a ƙafafunta.
Likitan da ya karɓi haihuwar wannan jaririya, ya bayyana cewar ta na cikin ƙoshin lafiya, kawai ta samu yawaitar waɗannan ƴan yatsun ne, sakamakon gadon halitta.
Tuni Iyalan da wannan jaririya ta fito daga cikinsu dai, su ke cigaba da bayyanata ga al’umma, inda su ke kiranta da sabuwar ‘Dholagarh Devi’, wacce wata fitacciyar mata ce da ta yi shura a fagen Ibada, duba da yadda wurin Ibadar ke kusa da inda aka haifi jaririyar.
Da ya ke bayyana matsayin lafiyarta, Likitan Asibitin da aka haifi wannan jaririya, Dr. BS Soni, ya ce “Babu wata illa dan an haifeta da yatsu 26, amma abin ta ɗauke shi ne daga ƙwayar halitta. Amma lafiyar yarinyar ƙalau.
Zuwa yanzu kuma, babu masaniyar ko Iyayen wannan jaririya za su miƙata ga sashen Tiyata domin rage yawan ƴan yatsun, ko kuma za su barta a yadda aka haifeta.