An Hana Wasu Ɗalibai Rubuta Jarrabawar Mock JAMB, Saboda Sun Saka Hijabi
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta bayyana irin rawar da ta taka ya yin da aka hana wasu Ɗalibai mata rubuta jarrabawar Gwaji ta JAMB Mock, a Jami’ar Covenant, da ke Otta, a jihar Ogun.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewar, an hana waɗannan Ɗalibai shiga Jami’ar mallakin Bishop David Oyedepo, domin rubuta jarrabawar ne, sakamakon sun sanya Hijabi.
Kuma tuni lamarin ke cigaba da yamutsa hazo a faɗin ƙasa, tsakanin ɗai-ɗaikun mutane, da ƙungiyoyi, inda kowa ke furta albarkacin bakinsa game da wariyar da aka nuna wa ɗaliban.
A martaninta, hukumar JAMB, ta ce tuni ta ɗauki mataki kan lamarin tun bayan da aka jawo hankalinta.
”An jawo hankalinmu kan wannan lamari, inda Jami’an da ke aikin bayar da tsaro, su ka hana wasu Ɗalibai shiga Jami’a, domin gudanar da jarrabawa, sakamakon umarnin da Jami’ar ta basu”.
”Sai dai, Jami’ar ta ce sam bata bada umarnin yin irin wannan cin zarafi ga Ɗaliban da su ka je rubuta jarrabawar ba.
”Kuma tuni Jami’an gudanarwar Cibiyar rubuta jarrabawar su ka garzaya zuwa bakin ƙofa, tare da shawo kan lamarin, inda kuma su ka tabbatar da cewar Ɗaliban sun shiga sun rubuta jarrabawarsu.
”Sai dai, rashin fara jarrabawar da wuri, ya sanya Ɗaliban basu kai ga kammala rubuta jarrabawar tasu ba, har lokaci ya ƙure”.
Da ta ke miƙa saƙon ban haƙuri, hukumar ta JAMB tace, za a sake bawa Ɗaliban damar rubuta wannan jarrabawa.
Ta kuma ƙara da cewar, ”Ya na da kyau Jama’a su sani, hukumar JAMB na yunƙurin samar da dai-daito a tsakanin Ɗaliban da su ka fito daga kowacce ƙabila, yanki, ko Addini”
Hukumar ta kuma sha alwashin ɗaukar dukkannin matakan da su ka dace, dan kiyaye aukuwar hakan, a nan gaba.