Ƙasashen Ƙetare

An Hangi Sarki Charles III A Karon Farko, Tun Bayan Kamuwarsa Da Ciwon Daji

An hangi fuskar Sarkin Burtaniya, Charles na III a karon farko, tun bayan gano yadda ya kamu da ciwon daji, a ranar Litinin.

An kuma hangi, yadda Sarkin da Sarauniya Camilla su ke barin gidansu na Clarence House, da ke birnin London, tare da nufar Fadar Buckingham.

Sarkin, ya bayyana cewar, har yanzu yana dauke da ciwon na Cancer, inda ya ke cigaba da karbar magani.

Jim kadan bayan faruwar hakan kuma, sai jirgin da ke dauke da Sarkin ya tashi daga Fadar Mulkin, zuwa gidansa da ke Sandringham.

Kafin hakan kuma, Yarima Harry ya isa birnin London domin ganawa da mahaifin nasa, sai dai babu tabbaci kan ko yana tare da shi har yanzu.

Masarautar ta Buckingham ce dai, ta fara bayyana kamuwar Sarkin da ciwon na daji, da ma yadda ya fara jinyar ciwon.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button