An Haramtawa Fasinjoji Amfani Da Jakar ‘Ghana Must Go’ A Filayen Jiragen Sama
Hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa (FAAN), ta haramtawa matafiya amfani da jakunkunan leda na ‘Ghana Must Go’, a filayen jiragen saman ƙasar nan.
Bayanin haramcin, na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ta FAAN, Henok Gizachew ya fitar, mai taken ‘Re: Prohibition Of Use Of Ghana Must Go’ a harshen Ingilishi, wato ‘Sake Tabbatar Da Haramcin Amfani Da Jakunkunan Ghana Must Go’ a harshen Hausa.
Sanarwar ta ce, haramcin ya shafi fasinjojin da ke bi ta filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa ne.
Dalilin da hukumar ta bayar na haramta amfani da jakunkunan kuwa shi ne, asarar da amfani da jakar ke haddasawa ga kamfanonin jiragen sama, ta hanyar lalata na’urar tantance kaya a filayen.
Tuni kuma shima kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines, ya sanar da haramtawa fasinjojinsa da ke nan Najeriya, amfani da jakunkunan samfurin ‘Ghana Must Go’, ta cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Nuwamban 2023, da ya aikewa Manajojin shiyya-shiyya na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman ta FAAN, inda kamfanin ya ce tsarin zai fara aiki ne, a ranar 25 ga watan na Nuwamba.