Ilimi

An Harbawa Ɗalibai Barkonon Tsohuwa, Ya Yin Zanga-Zangar Ƙarin Kuɗin Makaranta

Jami’an ƴan sanda sun yi awon gaba da biyu daga cikin Ɗaliban Jami’ar Lagos, tare da harba hayaƙi mai sa hawaye (teargas), a wurin da Ɗalibai ke gudanar da zanga-zangar ƙin jinin ƙarin kuɗin makaranta.

Lamarin dai ya faru ne, da tsakiyar ranar yau (Laraba), ya yin da ɗaliban Jami’ar Lagos ke tsaka da gudanar da zanga-zangar lumana, kan ƙarin kuɗaɗen Makarantar da Jami’ar ta yi.

Ɗalibai biyun da Jami’an ƴan sandan su ka yi awun gaba da su kuma su ne: Femi Adeyeye, da Philip Olatinwo.

Kuma tuni Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da aukuwar lamarin. Sai dai, ya ce ba shi da cikakken bayanin ɗalibai biyun da aka kama.

Tun da farko, Ɗaliban dai na zanga-zanga ne kan matakin da hukumar Makarantar ta ɗauka na ƙara kuɗaɗen Makarantar da Ɗalibai ke biya, daga Naira 26,000 da 76,000 zuwa tsakanin 120,750 da 240,250, wanda ya ke banbanta daga fagen karatu guda zuwa wani.

Bayan isar Jami’an ƴan sanda wurin ne kuma, sai su ka rarumi biyu daga cikin masu zanga-zangar tare da jefa su cikin Motar su Mai taken “Black Maria”, su ka kuma wuce da su zuwa Ofishin rundunar ƴan sanda na yankin.

Sai dai, a ya yin da aka aza ƙeyarsu, waɗanda aka kama ɗin, Adeyeye da Olatinwo, sun roƙi masu zanga-zangar da su cigaba da yi, kar su dakata.

“Wannan ba lokacin ja da baya bane. Yanzu dai ga mu a Motar ƴan sanda, muna masu tabbatar muku da cewar wannan shi ne farkon gwagwarmayar”, a cewar Ɗaliban, cikin wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Inda a nan ne kuma, Jami’an ƴan sandan su ka cigaba da harba Barkonon Tsohuwa a wurin, da nufin tarwatsa masu zanga-zangar.

Daman dai, kafin fara gudanar da zanga-zangar tasu, an hangi tarin Jami’an tsaro na SSS, Ƴan Sanda, Da ma LASTMA, a babbar ƙofar shiga Jami’ar.

Sai dai, ta cikin wani jawabi da ƙungiyar tabbatar da samun ingantaccen Ilimi ta ERC ta fitar, ta hannun Mataimakin Shugabanta, Isaac Ogunjimi, ta buƙaci Kwamishinan rundunar ƴan sandan Jihar, da “ya gaggauta sakin masu zanga-zangar, ba tare da ɓata lokaci, ko gindaya wani sharaɗi ba”.

Ƙungiyar, ta kuma ce kimanin masu zanga-zanga Uku ƴan sandan su ka cafke, ba biyu ba. Inda ta bayyana Ayodele Aduwo, a matsayin na ukun.

Ƙungiyar dai, ta ce wannan kamu da aka yi wa ɗaliban ba ya kan ƙa’ida (ya saɓawa doka), kuma tauye musu ƴancinsu ne.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button