Zamantakewa

An Kama Direban Motar Haya, Bayan Soka wa Jami’in Hukumar Zirga-Zirga Wuƙa

Jami’an hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Lagos (LASTMA), sun kama wani Direban Motar Haya, bisa zarginsa da sokawa Jami’in hukumar wuƙa, bayan da ya tare shi sakamakon karya dokar tuƙi, ranar Lahadi, a Lagos.

Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne, ta cikin wani jawabi da Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar ta LASTMA, Adebayo Taofiq, ya sanyawa hannu, a ranar Lahadi.

Direban wanda ba a bayyana sunansa ba, Jami’in ya tsare shi ne, bisa laifin ɗaukar fasinja a babbar hanya, wanda hakan ke haifar da cunkoson ababen hawan da ya kan kasance shiga haƙƙi ga sauran masu amfani da titin, a yankin Iponrin, na jihar Lagos.

Direban dai, “Ya yi ƙoƙarin tserewa, kafin daga bisani ya fito da wuƙa ya sokawa Jami’in.

“Bayan ya ga babban ciwon da ya ji masa da wuƙar, sai ya riƙe wuyansa, amma tuni Jami’an ƴan sanda daga Ofishin Iponri, su ka kama Direban”, a cewar jawabin.

Bayan kama shi kuma, an same shi da muggan makamai, da su ka haɗar da adda da wuƙa, a cikin motar hayar tasa ƙirar Volkswagen ‘T4’.

Gwamnatin jihar, ta kuma tabbatar da cewar, za a gaggauta hukunta Direban, domin hakan ya zama izina ga sauran bijirarrun direbobi irinsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button