An Kama Jagorar Zanga-Zangar Neman Sauƙaƙa Farashin Abinci, Tare Da Ƙarin Mutane 24
Rundunar ƴan sanda ta ƙasa, ta tabbatar da daƙume mutane 25 da ake zargi da kitsa zanga-zangar da wasu daga cikin al’ummar ƙasar nan su ka gudanar, a birnin Minna, na jihar Niger.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai, masu zanga-zangar kan tsadar farashin abinci a ƙasar nan, su ka mamaye birnin Minna, tare da rufe titin Minna zuwa Bada, da shatale-talen Kpakungu.
Ta cikin wani jawabi da Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Niger, Wasiu Abiodun ya fitar kuma, ya ce tuni rundunar ta daƙume wacce ta shirya zanga-zangar, Aisha Jibrin, tare da ƙarin wasu mutane 24 da ake zargin sun rufa mata baya.
A cewar Abiodun ɗin kuma, wasu daga cikin kayayyakin da aka samu a hannun waɗanda aka kama ɗin, sun haɗar da, Tsitaka, Wuƙaƙe Uku, Almakashi, Adda, har ma da saya (saw) guda ɗaya.
Sai kuma, Kayayyakin Maye, da gurayen da aka samu a hannun wasu daga cikinsu.
A ƙarshe, ya bayyana cewar, Kwamishinan ƴan sandan jihar, ya buƙaci ƴan Najeriya da su kasance masu bin doka.