An Kama Matashi Bisa Zargin Sace Na’urar Haske, A Masallaci
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta yi nasarar daƙume wani Matashi, bisa zarginsa da sace na’urar bada haske (Solar), tare da batirinta, a masallacin Juma’ar Hukunyi, da ke ƙaramar hukumar Kudan.
Da ya ke tabbatar da daƙume matashin, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce Jami’an rundunar tasu sun yi nasarar daƙume matashin mai suna, Basiru Rabi’u, da ke zaune a Sabon Gari, da ke Hukunyi ne, bayan tsaurara bincike kan ƙorafin da al’umma su ka shigar game da lamarin.
Tun da fari dai, jama’a sun lura da yadda matashin ya yi ta Safa da Marwa Marwa a kusa da farfajiyar Masallacin, kafin daga bisani ya faki ido, ya afka ciki.
Ɓarawon, ya kuma ce, ya na cefanar da kayayakin da ya sata ne, ga wani mutum mai suna, Mansir Umar, da ke ƙauyen na Nahuce.
Kakakin ya kuma ce, tuni rundunar tasu ta yi ram, da wanda ake zargi da sayen kayayyakin.