Zamantakewa

An Kama Matashin Da Ya Sayar Da Bidiyon Tsaraicin Wata Mata, Akan Naira 3,000

Rundunar ƴan sandan jihar Anambra, da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta daƙume wani matashi, bisa zarginsa da sayar da faifan bidiyon wata mata ga ƴan Social Media.

Matashin mai shekaru 20 a duniya, ana zarginsa ne da yin amfani da bidiyon tsaraicin matar wajen damfararta.

Chidinma Ikeanyionwu, da ke zama Mai taimakawa Kwamishiniyar Mata da bunƙasa walwala a jihar, Ify Obinabo, ita ce ta bayyana hakan ta cikin wani jawabi da ta fitar, a ranar Lahadi.

Inda ta ce, matashin ya fito ne, daga yankin Ndi Ikpa, da ke Ezinato, a ƙaramar hukumar Awka, ta jihar.

A cewar jawabin kuma, tun a watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki ne, Matar ta rasa ‘Memory Card’ ɗinta, wanda ke ɗauke da bidiyon nata na tsaraici.

Inda kuma, shi wanda ake zargin, ya tsinci memorin, tare da tuntuɓarta a watan Yuni ta wata kafar sada zumunta da ba a bayyana sunanta ba, inda ya buƙaci ta biya shi wasu maƙudan kuɗaɗe, domin ƙauracewa sakin bidiyon tsaraicin nata daga ɓangarensa.

Ita kuwa wannan Mata ta yi fumfurus tare da ƙin bashi kuɗaɗen da ya buƙata, inda hakan ya sanya wanda ake zargin ya yi yunƙurin ɗora bidiyon a dukkannin shafukan sada zumunta.

Duk kuma da buƙatar sa da Mijin Matar ya yi na ganin ya goge bidiyon, sai wannan Bawan Allah ya yi kunnen uwar shegu, tare da ɗora shi, a kafar Facebook, WhatsApp, da ma sauran Shafukan Sada Zumunta.

Ya kuma sayar da bidiyon ne a kan Naira 3,000 (Dubu Uku) ga ƴan midiya ɗin da su ka buƙata, kamar yadda bayanin ya bayyana.

Ikeanyionwu, ta kuma ce, tuni aka cika hannu da wannan Matashi mai aika-aika, jim kaɗan bayan da Matar ta shigar da ƙorafin aukuwar lamarin ga Kwamishiniyar, wacce ta yi gaggawar tuntuɓar rundunar ƴan sandan jihar, ta kuma buƙaci su cukumo shi.

Mataimakiyar yaɗa labaran, ta ce za a gurfanar da shi a gaban Kotun Majistirin sauraron ƙararrakin cin zarafi, da ke Awka.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button