Zamantakewa

An Karrama Alhaji Sani Bisa Bajintar Da Ya Nuna

Gamayyar wasu Matasa, ƙarƙashin Jagorancin Nuhu Umar, sun karrama Fitaccen Ɗan Jaridar nan, mamallakin Jaridar Rariya Online, Alhaji Sani Ahmad Zangina, da takardar girmamawa sakamakon bajintar da ya nuna.

Ta cikin wani saƙo da ya wallafa, ta shafinsa na kafar sadarwa ta Facebook, da tsakar ranar yau (Juma’a), Nuhu Umar ya ce, sun karrama Alhaji Sanin ne, sakamakon gurfanar da Mawaƙin Siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara, da ya yi, gaban Kotu, tare da ɗaukar nauyin Lauyoyi kimanin 10, domin su kare Jarumin Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, a wata shari’a da ake tsammanin Darakta a masana’antar, Alhaji Sheshe, zai maka shi, nan da sa’o’i 24 masu zuwa, muddin ya gaza fitowa ya bayar da haƙuri, a bai-nan-nasi.

“Mun karrama Alhaji Sani Ahmad zangina da babban lambar yabo wanda yakai RARARA kara a kotu sannan shine wanda ya dauki nauyin lauyoyi guda goma domin su kare AMDAZ wanda yan kungiyar kaniwood suka kai kara kotu akan yafaɗi gaskiyan irin ɓaɗalar da ƴan ƙungiyan fim na Hausa keyi.”, a cewar Nuhu Umar.

Ka zalika, ya jaddada cewar, a halin da ake ciki yanzu a Arewacin ƙasar nan, irin su Alhaji Sani Zangina ne su ka yi ƙaranci, duba da yadda babu abin da ya damu ƴan siyasa, face ranar zaɓe talakawa su kaɗa musu ƙuri’u kawai.

“A gaskiya a yanzu kaf arewacin najeriya bamuda irin sani Ahmad muna da yan siyasa amma babu ruwansu da damuwa da irin halinda zamu samu kanmu sudai damuwansu idan ranar zabe tazo kawai muzaɓesu”, a cewar Nuhu Umar.

Idan ba a manta ba dai, ko a ranar Alhamis ma, sai da Fitaccen Ɗan Jaridar ya fito ya bayyana sukarsa ƙarara, ga marasa kishin yankin Arewacin Najeriya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button