Labarai
An Karrama Gwamnan Nasarawa Da Lambar Yabo Ta FNSE
Ƙungiyar ƙwararrun Injiniyoyi ta ƙasa, ta karrama Gwamnan jihar Nasarawa, Engr. Abdullahi A. Sule, da lambar girmamawa ta FNSE.
An gudanar da bikin karramawar ne, a ya yin taron ƙungiyar ta Injiniyoyi na shekarar 2023, wanda ya gudana, a babban birnin tarayya Abuja.
Taron, mai taken: Sake haɓɓaka fannin ƙere-ƙere, domin bunƙasa tattalin arziƙi, ya samu halartar Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima GCON.
An kuma gudanar da bikin karramawar ne, a Cibiyar taro ta International Conference Centre, ranar Talata (28 ga watan Nuwamba, a babban birnin tarayya Abuja.