Nishaɗi

An Kori Mai Gabatar Da Shirin Talabijin, Doyin David Daga Bikin Bajakolin Taurari Na BBNaija

An yi wa fitacciyar mai gabatar da shirin Talabijin ɗin nan, Doyin David, tare da Kim Oprah korar kare, daga bajakolin fasahar taurari na BBNaija All Stars Show.

Hakan kuma na zuwa ne, ya yin da ya rage makonni Uku a ƙarƙare bajakolin reality show.

Korar Doyin dai, ya zo ne bayan da aka dakatar da ita daga Big Brother, bisa samunta da laifin furta kalaman cin zarafi, ya yin da musatayya ta yi zafi a tsakaninta da Abokiyar burminta, a ranar Alhamis. Inda ta ce za ta koma domin gabatar da bajakolin fasaharta, da ma cigaba da tallace-tallace.

Ya yin da ita kuwa, Kim Oprah, wacce ta je gidan a matsayin baƙuwa, ta nuna sha’awarta ga Cross, a ya yin da aka bata zaɓi tsakanin Pere da Cross, bayan korarta.

Za kuma a kammala bikin bajakolin fasahohin ne, a ranar 1 ga watan Oktoba, ya yin da dukkannin wanda ya kasance gwarzo a bikin, zai rabauta da kyautar Naira miliyan 120.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button