An Kuɓutar Da Masu Aikin Ginin Ƙasar India, Bayan Tsintar Kansu Cikin Halin Ƙaƙanikayi
An hangi fuskokin wasu Masu Aikin Gini a ƙasar India cikin murmushi da yammacin ranar Talata, bayan tsare su da aka yi tsawon kwanaki 17, a ya yin wani gangamin ceton alúmma da aka gudanar, bayan zargin fuskantar koma baya.
Alúmmar yankunan da maáikatan su ke, dangi, tare da muƙarraban Gwamnati dai, sun fito cikin wani salo na rera waƙoƙi da ke cewa, ‘Bharat Mata ki Jai’ harshen kasar na Hindi, wato ‘Muna yi wa kasarmu ta India fatan cigaba mai ɗorewa’ a harshen Hausa, ya yin da maáikatan su ke fita cikin faraá bayan likitoci sun duba su.
Ministan zirga-zirgar tituna da manyan hanyoyi na ƙasar, Nitin Gadkari, ta cikin wani faifan bidiyo da ya fitar ta kafar sada zumunta ta X, ya bayyana farincikinsa kan yadda maáikatan su ka Kuɓuta daga magarƙamar Silkyara, da ke Uttarkashi, wanda birnine da ke yankin jihar yammacin ƙasar ta Uttarkashi.
Maáikatan dai, sun kasance a rufe ne a inda aka tsare su, tun tsawon lokaci, sai dai ana basu abinci da ruwa ta hanyar bututu.
A yanzu haka kuma, sama da Likitoci goma sha biyu ne ke duba lafiyarsu.