An Liƙe Sammacin Kotu A Gidan Rarara
Wasu rahotanni daga majiya mai tushe, sun tabbatarwa da Jaridar Rariya Online, yadda Masinjan Babbar Kotun Mijistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, ya jagoranci liƙa takardar sammaci a gidan fitaccen Mawaƙin Siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, bayan da Kotu ta bada umarnin hakan.
An liƙe sammacin ne dai, da yammacin ranar Asabar, inda nan da nan kuma wasu mutane da ke aiki a gidan na Rarara, su ka yage takardar, tare da wanke bangon gidan.
Wani Ɗan Jarida Mai suna, Alhaji Sani Ahmad Zangina ne dai, ya yi ƙarar Rararan, a gaban Kotu, bisa zarginsa da furta kalaman tunzura al’umma, bayan da ya zargi Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da yin dama-dama da ƙasar nan, kafin miƙata ga shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kuma tuni Kotu ta fara sauraron shari’ar a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, amma wanda ake ƙara, bai bayyana a Kotun ba, sakamakon ƙin karɓar takardar sammaci da ya yi, ya yin da Masinjan Kotun ya halarci gidansa, domin damƙa masa takardar, wanda hakan ne ma ya sanya Kotun bada umarnin liƙa masa takardar sammacin a gidansa.