Wasanni

An Naɗa Finidi George A Matsayin Sabon Mai Horas Da Ƴan Wasan Super Eagles

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF), ta sanar da naɗin, Finidi George, a matsayin sabon mai horas da ƴan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles.

NFF ta ce, naɗin na George ya zo ne bayan tantance shi, da Kwamitin hukumar ya yi.

NFF, ta kuma sanar da naɗin nasa ne, a yammacin ranar Litinin.

George, ya shafe tsawon watanni 20 a matsayin Mataimakin Tsohon Kocin Ƴan Wasan, Jose Santos Peseiro, kafin Peseiro ɗin wanda ɗan asalin Portugal ne ya yi bankwana da matsayinsa, bayan kammala gasar Kofin Ƙasashen Afirka, wanda aka gudanar a ƙasar Cote D’Ivoire, da kuma jagorantar tawagar a wasannin sada zumunci biyu da ta fafata watan da ya gabata, a ƙasar Morocco.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button