Ilimi
An Naɗa Sabon Uban Jami’ar Bayero
Gwamnatin tarayya ta nada Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, a matsayin Uban Jamiár Bayero (Chancellor), da ke jihar Kano.
Takardar nadin wacce ke dauke da sa hannun babban Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ta sanar da amincewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan nadin na Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, a matsayin Uban Jamiár.
Inda sanarwar ta kuma kara da bayyana cewar shugaban a yanzu zai kasance mai kakkarfar alaka da Jamiár, tare da kasancewaa saman dukkannin shuwagabanni, dalibai, da ma maáikatan da ke Jamiár, kuma a duk lokacin da ya ke nan shi ne zai dinga Jagorantar babban taron Jamiár.