Labarai
An Saki Matar Da Ta Saci Riga, Bayan Shafe Watanni 8 A Gidan Gyaran Hali
Wata Mata mai suna, Zuwaira Yusuf, ta shaƙi iskar ƴanci, daga gidan ajiya da gyaran hali, na Hong, da ke ƙaramar hukumar Hong, ta jihar Adamawa, bayan shafe tsawon watanni takwas ta na ɗiban gabza, bisa aikata laifin satar Rigar Sawa, da Kwanon Sanyayawa da Riƙe zafin Abinci (Cooler).
Tun da farko, Kotun Majistirin ƙaramar hukumar Gombi ce dai, ta yankewa matar hukuncin zaman gidan waƙafi na tsawon shekaru biyu.
Zuwaira, ta kuma shaƙi iskar ƴancin ne, bayan da Kwamitin Shari’a (JDC) ƙarƙashin jagorancin, Mai Shari’a Hafsat Abdulrahman, su ka kai ziyara gidan gyaran halin da Matar ta ke ɗaure.