An Saki Sakamakon Jarrabawar NECO Nuwamba/Disamba 2023
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun Sakandire ta ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarrabawar External (Private) NECO ta shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Dantani Wushishi shi ne ya sanar da sakin sakamakon, ya yin wani taron Manema Labarai da aka gudanar, ranar Litinin, a birnin Minna, na jihar Niger.
Wushishi, ya ce kimanin Ɗalibai 74,950 ne su ka yi rijistar jarrabawar, ya yin da kimanin 39,213 wanda ke wakiltar kaso 52.31 su su ka kasance Maza, sai kuma 35,737 da ke wakiltar kaso 47.68 da su ka kasance Maza.
Kimanin Ɗalibai 50,066 ne kuma su ka samu Credits a darussan Turanci da Lissafi, wanda hakan ke wakiltar kaso 67.35 na ɗaukacin ɗaliban.
A warware kuma, jimillar Ɗalibai 55,272 ne su ka samu nasara a darasin Turanci, wanda hakan ke wakiltar kaso 75.59 na ɗaliban.
Ya yin da kimanin Ɗalibai 67,815, da ke wakiltar kaso 92.75 kuwa, su ka samu nasara a darasin Lissafi.
Bugu da ƙari an samu Cibiyoyin jarrabawa 2 da laifukan satar jarrabawa, a jihohin Kaduna da Ogun.