An Saki Sakamakon POST-UTME, Na Jami’ar YUMSUK
An Saki Sakamakon POST-UTME, Na Jami’ar YUMSU
An saki sakamakon jarrabawar POST-UTME ta Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da ke birnin Kano (YUMSUK), wacce aka rubuta a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, 14 ga watan Satumban da mu ke ciki, domin bada guraben karatu a Jami’ar, a kakar karatu ta 2023/2024.
A yanzu dai, Ɗalibai za su iya duba sakamakon jarrabawartasu, idan su koma shafinsu na makarantar (Post-UTME Portal) akan: https://yumsuk.edu.ng/screening/index.php, su ka sanya Registration Numbers ɗinsu, Sannan su yi Login, tare da danna maɓullin ‘PUTME Result’, da zarar shafin ya buɗe, domin ganin sakamakon jarrabawoyinsu.
Post-UTME dai, ita ce matakin tantancewa na biyu, da ake yi wa ɗalibai kafin basu guraben karatu, bayan rubuta jarrabawar UTME, a karon farko.
Allah ya sa a ga sakamako mai kyau.
MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956.