Ilimi
An Saki Timetable Ɗin NECO SSCE
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun Sakandire ta ƙasa (NECO), ta saki jadawalin lokutan rubuta jarrabawar ta wannan shekarar (Timetable 2024), wanda hakan ke alamta ƙaratowar lokacin fara rubuta jarrabawar a faɗin Najeriya.
Bayanin sakin timetable ɗin, na ɗauke ne ta cikin wani saƙo da hukumar ta wallafa ta shafinta na X, a ranar Litinin.
Inda jadawalin, ya nuna cewar za a fara rubuta jarrabawar ne, a ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, a kuma kammala a ranar Juma’a, 26 ga watan Yulin 2024.
Ga hotunan Timetable ɗin nan, a ƙasa 👇
Domin Neman Ƙarin Bayani, Ku Tuntuɓi: Miftahu Ahmad Panda, akan: 08039411956.