Kasuwanci

An Samu Tashin Gobara A Tashar Lantarkin Kano

Babbar tashar rarraba hasken wutar lantarki ta jihar Kano, da ke Ɗan Agundi, ta kama da wuta, da yammacin Lahadi.

Cibiyar kuma, ita ce babbar tashar da ke bada hasken lantarki, ga mafi yawan sassan birnin jihar.

Gobarar tayi sanadiyyar ƙonewar taransifomomi da dama, tare da ƙarin wasu kayayyakin lantarkin da ke tashar.

Hukumar gudanarwar kamfanin rarraba hasken lantarki (TCN) ta bayyana cewar, transformer biyu kawai lamarin ya shafa, domin kuwa sauran biyu su na cikin kyakykyawan yanayi.

“Ba na ofishi lokacin da lamarin ya faru, amma Jami’an da ke wurin sun tabbatar min cewar, transformer biyu lamarin ya shafa, ɗaya tana cigaba da aiki. Akwai wata guda ɗaya ma da bata fara aiki ba, ita ma gobarar bata shafeta ba”. a cewar Jami’in.

Da aka tambaye shi cewar, ko duk da hakan za a cigaba da bada hasken lantarki daga tashar ?, Jami’in ya ce, “hakan ba zai dakatar da rarraba hasken lantarki ba, tun da guda ɗaya tana aiki. Amma dai, a yanzu an kashe ta, za a dawo da wuta da zarar komai ya dai-daita”.

Tuni kuma hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta samu nasarar murƙushe gobarar, duk da dai an gaza samun Kakakin rundunar, Saminu Yusif Abdullahi, ta wayar tarho, har ya zuwa lokacin da mu ke haɗa wannan rahoto.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button