An Sanya Dokar Hana Fita A Kano, Bayan Da Al’ummar Jihar Su Ka Shiga Cikin Halin Fargaba
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta sanar da sanya dokar hana fita a jihar, biyo bayan tashe-tashen hankulan da aka fara fuskanta, tun bayan zartar da hukuncin Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta yi.
Rundunar ta sanar da ɗaukar wannan mataki ne, ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan rundunar ƴan sandan Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, ya sanyawa hannu, da yammacin Laraba.
Dokar kuma, za ta yi Aiki ne tsawon sa’o’i 24, inda ta fara Aiki daga ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Laraba, zuwa 6:00 na yammacin Alhamis.
Rundunar ta kuma bayyana cewar, ta sanar da Gwamnatin Kano wannan mataki da ta ɗauka, ta cikin wata sanarwa da ta aike mata.
Rundunar ta kuma ce, Jami’anta, tare da Jami’an sauran hukumomin tsaro, za su cigaba da gudanar da zagayen kuturunka nawa a lungu da saƙon jihar, dan tabbatar da Jama’a sun yi biyayya ga wannan doka.
Ka zalika, Sanarwar rundunar ta yi kira ga Mazauna jihar, da su bawa hukumar haɗin kai, tare da gargaɗin masu kunnen ƙashin da ka iya karya dokar, ta na mai tabbatar da cewar, za ta tabbatar da dukkannin wanda aka samu da yi wa dokar karantsaye ya fuskanci hukunci.