Labarai

An Sanya Lokacin Rantsar Da Sababbin Majalissun Tarayya, Ya Yin Da Wa’adin Tsofaffin Zai Cika, A Wannan Makon

Majalissun tarayya na tara, waɗanda aka rantsar, tun a ranar 11 ga watan Yunin 2019, za su kawo ƙarshen wa’adin su a makon nan.

Inda Majalissar wakilai za ta kawo ƙarshen nata zaman, a ranar Talata, ya yin da Majalissar Dattijai kuwa, ake sa ran za ta ƙarƙare, a ranar Laraba.

Kuma ana sa ran Shugaban majalissar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan ne zai rufe zaman Majalissar, ya yin da Shugaban Majalissar wakilai, Femi Gbajabiamila, shi ma zai rufe tasu majalissar, a ranar Alhamis.

Bayanin hakan kuma, ya fito ne, ta bakin shugaban majalissar ta wakilai, Femi Gbajabiamila, a ya yin da ya ke bayyana aikace-aikacen da za su gudanar, a makon da mu ke ciki.

Ana kuma sa ran, za a rantsar da sababbin Majalissun tarayya na 10 ne, a ranar 13 ga watan Yunin da mu ke ciki, inda anan ne za a zaɓi sababbin Shuwagabannin Majalissun.

Gabanin rantsar da Majalissar dai, tuni sassa daban-daban ke fafutukar ganin sun shugabanceta, daga ɓangaren majalissar Dattijai, zuwa ta Wakilai.

Inda kwamitin gudanarwar jam’iyya mai mulki ta APC, ya amince da tsarin raba shugabancin zuwa shiyya-shiyya, tun a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata, bayan da ya amince da Sanata Godswill Akpabio, daga jihar Akwa Ibom, da ke yankin Kudu maso Kudancin ƙasar nan, a matsayin Shugaban Majalissar, tare da Sanata Barau Jibrin, daga jihar Kano, da ke yankin Arewa maso yamma, a matsayin mataimakinsa; Sai kuma Tajudeen Abbas, daga jihar Kaduna, da ke yankin Arewa maso yamma, a matsayin Shugaban majalissar wakilai, Ya yin da Benjamin Kalu, daga jihar Abia, da ke yankin Kudu maso Gabas, zai zame masa mataimaki.

Sai dai wancan zaɓi na jam’iyyar APC, na cigaba da samun suka (ƙin amincewa), daga waɗanda ke adawa da tsarin.

Daga cikin waɗanda ke neman sahalewar ɗarewa karagar Shugabancin Majalissar Dattijan dai, akwai Orji Uzor Kalu, daga jihar Abia; Sai tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari; da Sanata Sani Musa, na jihar Niger.

A majalissar wakilai kuwa, masu neman Shugabancin sun haɗar da, Tsohon Mataimakin Shugaban Majalissar, Ahmed Wase; Sai Shugaban Kwamitin Sojojin ruwa na Majalissar, Yusuf Gagdi; Aliyu Betara; Sai shugaban kwamitin kula da albarkatun ruwa, Sada Soli; Chinedu Ogah; Miriam Onuoha; da Sani Jaji.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kuma, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Shugaban majalissar wakilai, Femi Gbajabiamila, wanda ya shafe zango Shida a majalissar, a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Yuni (bayan rushe majalissar).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button