Ilimi
An Sanya Lokacin Rijistar JAMB Ta Shekarar 2024
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa, JAMB, ta sanar da lokacin rijista, tare da rubuta jarrabawar JAMB (UTME), a yau (Laraba).
Za a fara rijistar JAMB UTME ne, a ranar 15 ga watan Janairu (January) na shekarar 2024, ya yin da za a rufe, a ranar 26 ga watan Fabrairu (February).
Za kuma a rubuta jarrabawar gwaji ta Mock-UTME, a ranar 7 ga watan Maris ɗin 2024.
Za kuma a rubuta jarrabawar ta JAMB UTME, daga ranar 19 zuwa 29 ga watan Afrilun 2024.
Ana kuma sa ran, fara cire Slip ɗin Jarrabawa, daga ranar 10 ga watan Afrilu.
✍️MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956