Ilimi
An Sanya Ranar Gudanar Da Jarrabawar Shiga School Of Nursing, Kano
Hukumar gudanarwar Kwalejojin Aikin Jinya, na Jihar Kano, na sanar da dukkannin Ɗaliban da su ka nemi makarantun Ayyukan Jiyya Da Unguzoma (Nursing & Midwifery), da ke Kano, Ɗambatta, da ma Gwarzo, a kakar karatu ta 2023/2024 cewar, za a gudanar da jarrabawar tantancewa, ta hanyar na’ura maiƙwaƙwalwa (CBT), a ranakun Laraba 17 ga watan Mayu, zuwa Juma’a 19 ga watan na Mayu, a Cibiyar jarrabawar na’ura mai ƙwaƙwalwa, da ke Kwalejin a Kano (College Computer Centre, Kano).
Saboda haka, ana buƙatar dukkannin Ɗaliban da su ka nemi waɗannan makarantu, da su halarci Cibiyar a waɗannan ranaku, ɗauke da Acknowledgement Slips ɗinsu, da ma shaidar biyan kuɗi (Evidence Of Payment).