Kasuwanci
An Shawarci Najeriya Kan Fara Sayar Da Ɗanyen Mai A Farashin Naira, Domin Farfaɗo Da Darajar Kuɗinta
Fitaccen masanin harkokin kuɗi, Ikechukwu Unegbu, ya shawarci Gwamnatin Tarayya, da ta duba yiwuwar fara sayar da ɗanyen man da take haƙowa a farashin Naira, a wani mataki na ganin ta bunƙasa darajar kuɗaɗen ƙasar.
Unegbu, wanda tsohon shugaban Cibiyar Ma’aikatan Banki ta Najeriya ne, ya bayyana hakan, a yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, ranar Lahadi, a babban birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, ɗanyen man babban Abu ne da zai ɗaga darajar kuɗin ƙasar, muddin aka yi amfani da Naira wajen sayar da shi a kasuwar duniya.
Ya kuma ce, akwai buƙatar Gwamnatin ta yi watsi da tsarin OPEC, ta hanyar fara sanya farashin manta akan kuɗin Naira.