An Shirya Horon Kwanaki Uku Ga Jarumai Da Masu Bada Umarnin Fina-Finai, Bayan Taron KILAF
Kwamitin shirya Bikin Bajakolin Fina-Finan Nahiyar Afirka na shekarar 2023, da ake gudanarwa a jihar Kano, KILAF, ya shirya bita ga Jaruman Fina-Finai da Masu Bada Umarni, a cibiyar bada horon sanaóí ta Dangote, da ke Sabuwar Jamiár Bayero.
An kuma, gudanar da shirin mai taken ‘Jarumta a Gaban Naúrar Ɗaukar Hoto ne tsawon kwanaki uku’.
An kuma shirya bada horon ne bisa manufar haɗa Jarumai da Masu Bada Umarni a Masanaántar shirya fina-finai, domin nusantar da su kan manufar samar da masanaántar, da ma rawar da ya cancanci ta taka.
Sani Muázu, Galadiman Jos, wanda ya kasance guda daga cikin masu bada horo a ya yin bitar, ya ce masanaántar shirya fina-finai ta shafe tsawon shekaru a Najeriya, ya na mai alamta yadda aka kafa masanaántar tun kafin samun ƴancin ƙasar nan.