An Tilastawa Ɓarayi Shanye Giyar Da Su Ka Sata, A Afirka Ta Kudu
Wani faifan bidiyo, da ke cigaba da tashe a shafukan sada zumunta na zamani, ya nuna yadda aka tilastawa wasu ɓarayi shanye giyar da su ka sata, a wani shago, da ke ƙasar Afirka ta Kudu.
Wani Ɗan Jaridar ƙasar ta Afirka ta Kudu, mai suna, Velani Ludidi ne dai, ya wallafa faifan bidiyon yadda ɓarayin su ka fasa kanti, tare da sato giyar.
Inda ya ce, bayan kama ɓarayin washe gari ne kuma, sai mamallakin shagon ya tilasta musu shanye dukkannin giyar da su ka sata, ko kuma su fuskanci hukuncin gurfana a gaban Kotu.
“Ɓarayin sun karya ƙofar shagon ne, inda su ka saci giyar wacce ta kai kimanin Dubu 14. An kuma kamasu washe gari da giyar. Sai mai shagon yace dole su shanyeta baki ɗaya a lokaci guda, ko kuma su fuskanci hukuncin shari’a. Ɓarayin su na ganin ta kansu,” a cewarsa.
Ta cikin faifan bidiyon kuma, an hangi yadda ɓarayin su ke kwankwaɗar kwalaben giyar.