Wasanni

An Tsallake Wata Ƴar Wasa Ya Yin Bada Kyaututtuka A Ireland, Saboda Kasancewarta Baƙar Fata

Wani fai-fan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta na zamani, wanda ke nuna yadda aka tsallake wata ƴar wasa baƙar fata, a ya yin bada Kyaututtuka ga zakarun gasar Irish, ya jawo cece-kuce.

Faifan bidiyon, wanda aka ce an ɗauke shi ne, a watan Maris ɗin shekarar 2023, ya nuna yadda ƴan wasan da su ka yi nasarar su ka jeru, su na jiran a basu kyaututtukan karramawarsu, amma abin mamaki sai aka tsallake wata yarinya baƙar fata, a ya yin rabon kyautar karramawar, ya yin da aka bawa sauran ƴan wasa ƴan uwanta, da su ka kasance fararen fata.

Bayan bidiyon ya zagaye kowacce kafar sadarwa a wannan makon kuma, sai sashen bada shaidar karramawar na Ireland, ya fitar da sanarwar bada haƙuri kan aukuwar lamarin, bayan da ita ma yarinyar ta zargi hakan a matsayin wariyar launin fata.

Hukumar wasannin, ta kuma ce, tuni aka shawo kan lamarin, tun a watan Augusta, amma Mahaifiyar yarinyar ta ƙi bada haɗin kai, ta na mai cewar, Iyalinsu basu karɓi saƙon ban haƙurin ba.

Gymnastics Ireland, sun ce, sun samu tattaunawa da Matar, wacce a yanzu ba memba bace a hukumar ta wasanni, bayan da ta ƙi amincewa da sake sabunta takardar kasancewarta a matsayin memba.

Hukumar wasannin dai na cewa, “Bayan gano kuskuren da aka aikata, hukumar wasanni ta bada haƙuri ga ƴar wasar cikin gaggawa, tare da bata kyautar karramawarta tun a wurin.

“Masu ruwa da tsaki, sun kuma bayyana nadamarsu bisa aukuwar wannan lamari, wanda su ka bayyana a matsayin rashin gaskiya, kuma su ka miƙa saƙon ban haƙuri, gare ta da iyalanta baki ɗaya. Amma Mahaifiyarta ta yi watsi da hakan.

“Bayan jerin tattaunawar, Gymnastics Ireland da Iyayen yarinyar, sun ce ba za su sake shiga cikin tsarin gasar ba, za kuma su nemi shawara a shari’ance”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button