An Tsare Wani Mutum A Gidan Gyaran Hali, Saboda Sayen Awakin Sata, A Kano
Kotun Majistiri, da ke Kano, ta aike da wani mutum mai suna, Buhari Sani, mazaunin ƙauyen Gafan, da ke ƙaramar hukumar Garin Malam gidan gyaran hali, bisa zarginsa da sayen Awakin Sata, da kimarsu ta kai Naira miliyan 5, da ake zaton an sato su ne daga Fulani makiyaya.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ce kuma, ta gurfanar da Sanin, a gaban Kuliya, bisa tuhume-tuhume guda biyu, da su ka haɗar da Cin Amana, da Sayen Kayan Sata.
Inda mai gabatar da ƙara, Asmau Ado, ta ce laifukan sun saɓawa sassa na 97 da 247, na kundin Penal Code.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Mustapha Saad Datti, ya kuma aike da mutumin zuwa gidan gyaran hali, bayan musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa da ya yi, tare da ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan gobe, na Yuli.