Zamantakewa

An Yi Wa Mutumin Da Ya Sace Sabulun Kakarsa Afuwa, Bayan Shafe Kwanaki 120 A Gidan Waƙafi

An saki wani mutum mai suna, Hassan Ahmadu, daga gidan gyaran hali, bayan da ya shafe kwanaki 120 a gidan, sakamakon sace sabulu da wasu ƴan kuɗaɗen kakarsa ta wajen Uwa.

Babbar Kotun Maiha, da ke Jihar Adamawa ce dai, ta yankewa Ahmadu hukuncin ɗaurin shekaru biyu, a gidan na gyaran hali, tun fiye da watanni huɗu da su ka gabata.

An kuma sake shi ne, a ranar Litinin, bayan da Kwamitin gidan gyaran hali, ƙarƙashin Jagorancin Babbar Jojin Jihar, Hapsat Abdulrahman, ya kai ziyara gidan gyaran halin Maiha, da ya ke ciki.

Al’umma da dama kuma, na kallon wannan hukunci a matsayin gani ga wane, Wanda Hausawa ke cewa, ‘Ya ishi wane tsoron Allah!’.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button