Siyasa

An Zaɓi Danladi Jatau A Matsayin Sabon Shugaban Majalissar Dokokin Nasarawa

A yau (Juma’a) ne, membobin Majalissar Dokokin jihar Nasarawa, su ka zaɓi Ɗan Majalissa, Danladi Jatau, wanda ke wakiltar Kokona ta Yamma (Kokona West) a matsayin shugaban majalissar.

Ya yin da su ka amince da Mohammed Oyanki, da ke wakiltar yankin Doma Ta Arewa (Doma North), a matsayin mataimakin shugaba.

Zaɓar sababbin shuwagabannin kuma, na zuwa ne, bayan da a ranar Talatar da ta gabata, Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta ƙwace nasarar da tsohon shugaban majalissar ya samu, a ya yin zaɓen watan Maris.

Shugaban Majalissar, Danladi Jatau na jam’iyyar APC, ya haɗa kai da Oyanki na PDP ne, inda su ka tsaya takarar shugabancin Majalissar, tare da samun nasara, domin bayyana tsantsar haɗin kai, da zaman lafiyar da Majalissar ke ciki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button