Ana Daf! Da Samun Tsayayyiyar Wuta, A Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na jihar Kano (KEDCO), ya bayyana shirinsa na fara bada wutar lantarki tsawon sa’o’i 24 a jihohin Kano, Katsina da Jigawa, da zarar an kammala aikin sababbun turakun wutar lantarki.
Hakan kuma ya zo ne, sakamakon Shirin kamfanin na bunƙasa wutar lantarkin da ya ke samarwa zuwa MegaWatts 200, da zarar an kammala aikin turakun lantarkin da za su samar da MegaWatts 100 na lantarki.
Shugaban zartarwar kamfanin, Adamu Gumel, shi ne ya yi wannan albishiri, a ƙaramar tashar wutar lantarki ta Zawaciki, da ke ƙaramar hukumar Kumbotson jihar Kano.
Ta cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa ta shafinsa na X a ranar Alhamis dai, Gumel ya ce, “nan gaba kaɗan, za ku ga yadda waɗannan ƙananun tashoshin lantarkin sun wadaci ko ina, a jihohin da mu ke kula da su na Kano, Katsina da Jigawa, wanda hakan zai bunƙasa yawan wutar lantarkin da mu ke samarwa abokanan mu’amalarmu”.