Ana Shirye-Shiryen Samar Da Hukumar Hisbah A Jihar Yobe
Majalissar dokokin Jihar Yobe, ta fara gudanar da taron jin ra’ayin Jama’a, kan wasu ƙudure-ƙuduren dokoki guda biyu, na samar da hukumar Hisbah, da ma hukumar bunƙasa Fasahar Sadarwa, a Jihar.
Shugaban Majalissar, Chiroma Buba, shi ne ya sanar da hakan, a ya yin da ya ke buɗe taron jin ra’ayin Jama’ar, ranar Alhamis, a birnin Damaturu.
Inda ya ce, dukkannin ƙudurorin dokokin guda biyu, sun samu nasarar tsallake karatu na farko, da na biyu, inda aka damƙa su a hannun kwamitocin Majalissar, domin ɗaukar matakai na gaba.
Buba, ya kuma yabawa ƴan Majalissar bisa bijirowa da waɗannan ƙudurorin dokoki, muhimmai guda biyu.
“Insha’Allahu Hisbah za ta tsaftace Jihar nan, daga dukkannin nau’o’in ayyukan rashin tarbiyya, a cikin zamantakewarmu.
“Ita kuma hukumar bunƙasa fasahar Sadarwar za ta bada gudunmawa matuƙa wajen samarwa da matasanmu Ayyuka”, a cewarsa.
A jawabinsa tun da farko, Shugaban Kwamitin Shari’a da Al’amuran Addinai na Majalissar, Yakubu Suleiman, roƙon Mahalarta taron ya yi da su bada tasu gudunmawar wajen tabbatar da nasarar waɗannan ƙudurorin dokoki guda biyu.