Ana Zargin Hukumomi Da Aikata Kura-Kurai, A Rijistar Masu Zaɓen Zimbabwe
Ɗan takarar shugabancin kasar Zimbabwe, daga tsagin jamiyyun adawa ya yi kira ga shugaban kasar, Emmerson Mnagagwa da ya sanya lokacin gudanar da manyan zabukan kasar
Nelson Chamisa ya kuma yi wannan kira ne bayan da ya tabbatar da sanya sunansa daga cikin sahun masu zabe, sabanin korafin da masu zaben kasar da dama ke yi, na bacewa, ko cire sunayensu daga cikin jadawalin masu kada kuriár.
Jamíyyar da Chamisa din ya fito, ta CCC dai, a ranar Litinin ta bayyana cewar jadawalin masu kada kuriár da hukumomin zabe su ka bayyanawa jamaá dai, na cike da kura-kurai.
Ka zalika, shima wani dan majalissa, daga jamíyyar ta CCC, wanda kuma ya kasance tsohon Ministan Ilimi, ya ce ya na daga cikin masu kada kuriún da su ka rasa sunayensu a jadawalin da aka like, a cibiyoyin kada kuriá.
Inda daga baya kuma, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewar, ya tsinci sunan nasa, a wata cibiyar kada kuriá ta daban, da ke da nisa da inda gidansa ya ke.
Inda ya kuma bayyana cewar, daruruwan alúmma ne ke fuskantar irin matsalar tasa.
Inda ya shawarci hukumomin zabe da su gyara dukkannin kura-kuran da ke cikin jadawalin na yanzu.