Labarai

Ana Zargin Masu Ginin Gidan Yari Da Sace Rodi

An kama wasu huɗu daga cikin ma’aikatan da ke aikin ginin gidan gyaran halin Ilesa, a jihar Ogun, bisa zarginsu da sace rodin aikin.

Wani jami’in tsaro, wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya bayyanawa Manema Labarai a ranar Asabar cewa, ma’aikatan sun fice da rodin ne daga farfajiyar da ake ginin.

Sai dai, gungun wasu Mafarauta, tare da Jami’an tsaron daji, sun yi nasarar yin ram da Motar da Ma’aikatan su ka loda ƙarafen Rodin, ya yin wani atisaye da su ka gudanar, a yankin Owode, da ke Ede.

Wani faifan bidiyo da ke bayyana yadda Jami’an ke tuhumar ma’aikatan bayan kama su dai, ya hasko yadda guda daga cikinsu ke musanta aikata laifin, bayan da ya ce shi Direban Motar da aka ɗauko Rodin ne kawai.

Su kuwa sauran guda ukun, Injiniyoyi ne a aikin ginin, ya yin da guda biyu kuwa su ka kasance masu zanen wurin.

Tuni guda daga cikin waɗanda ake zargin, mai suna, Kehinde ya amince da aikata laifin, ya na mai bayyana cewar yanayin matsin da ake ciki ne, ya tilasta musu runtuma satar.

Kwamandan rundunar tsaro ta NHFSS, Ahmed Nureni, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne da yammacin ranar Alhamis, a Owode, Ede, da ke kan titin Gbongan zuwa Osogbo.

Ka zalika, shi ma Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da cewar, waɗanda ake zargin, a yanzu haka, su na tsare a komar hukumar, lnda ake cigaba da gudanar da bincike.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button