APC Ta Ƙyanƙyashe Ƙoyaye 11 A Jihar Gombe
Jam’iyyar APC, ta lashe zaɓen shuwagabannin ƙananan hukumomi, a dukkannin ƙananan hukumomi 11, na jihar Gombe.
Ka zalika, ta lashe zaɓen ɗaukacin Kansiloli 114, da ke mazaɓun jihar, a zaɓen da aka gudanar, a yau (Asabar).
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Gombe, Malam Saidu Awak, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen jihar, ya kuma ce jam’iyyu biyar ne kacal suka iya fitar da ƴan takarkaru, daga cikin jam’iyyu 19, da ke da rijista a jihar.
Awak, ya kuma bayyana cewar, jam’iyyar APC ce kawai, take da ƴan takarkarun Kansiloli, a dukkannin mazaɓun jihar 114.
Da yake martani kan sakamakon zaɓen, shugaban jam’iyyar Accord na jihar, Alhaji Mohammed Garba, yace jam’iyyarsa ta shiga an dama da ita a zaɓen, domin ƙara jaddada kasancewarta, a jihar.
Garba, ya kuma taya waɗanda suka samu nasarar lashe zaɓen, murna, gami da fatan alkairi.