Siyasa

APC Ta Maka Kwamishinan Shari’a Na Kano A Gaban Kwamitin Ladabtar Da Lauyoyi

Jam’iyyar APC, reshen jihar Kano, ta shigar da ƙarar Kwamishinan Shari’a kuma Atoni Janar na jihar, Haruna Isa Dederi, a gaban Kwamitin Ladabtarwa na ƙungiyar Lauyoyi ta ƙasa, bayan da ya zargi Alƙalan da su ka yi hukuncin shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta Kano, da karɓar rashawa.

Ta cikin ƙarar, wacce shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya shigar ranar Lahadi, jam’iyyar ta zargi Kwamishinan da bayyana zargin karɓar na goro ƙarara akan Alƙalan Kotun ɗaukaka ƙara da ke babban birnin tarayya Abuja, ta cikin wata tattaunawa da ya gudanar, a tashar Talabijin.

An kuma aike da wasiƙar ne zuwa ga shugaban ƙungiyar ta NBA, Yakubu Maikyau, da shugabanta reshen jihar Kano, Sagir Gezawa, inda kuma aka aikewa da shima Dederi ɗin kwafinta.

Cigaban kuma na zuwa ne, kwana guda bayan da wata ƙungiya ita ma ta yi kira ga NBA ɗin da ta ladabtar da Dederi, da dukkannin sauran membobinta da ke yunƙurin wuce gona da iri.

Ta cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Laraba, a kafar Talabijin ta Channels, cikin shirin ‘Sunrise Daily’ dai, an hangi yadda Kwamishinan ke nuna rashin jindaɗinsa kan yadda Alƙalan Kotun ɗaukaka ƙara su ka sake sauke Gwamna Abba Kabir Yusuf daga kan kujerar Gwamnatin jihar, da ma yadda fannin na shari’a ke cigaba da taɓarɓarewa a Najeriya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button