Ilimi

ASUU Ta Yi Hannunka Mai Sanda Kan Yawaitar Ajiye Aikin Malaman Jami’o’i

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta ankarar da Gwamnati da alúmma kan yadda Malamai ke yawan ajiye ayyukansu, daga Jamióín ƙasar nan.

Ƙungiyar ta ce da yawan ɓangarori, da sassan Jami’oí su na fuskantar ƙarancin Malamai, sakamakon ajiye ayyukan da malaman jami’oín ke yi, domin neman ayyuka masu gwaɓi.

Ƙungiyar ta kuma ce jinkirin biyan albashi, rashin biyan alawus, ƙarancin kayayyakin aiki, da ma rashin girmama Malamai na daga cikin abubuwan da su ke jawo ajiye aikin Malaman Jami’o’in a ƴan watannin da su ka gabata.

Shugaban ƙungiyar ASUU reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, wanda ya yi bayanin jiya a Ibadin, ya ƙara da cewar, Jami’oin Gwamnati su na cikin halin ƙaƙanikayi, ya yin da su ke cigaba da rasa Malamansu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button