Ba a Samu Mai Tsayawa Takarar Sakataren Kuɗi Ba, Ya Yin Da Aka Rantsar Da Sababbin Shuwagabannin NUJ Na Yobe
Ƙungiyar Ƴan Jaridu Ta Ƙasa, reshen jihar Yobe, ta rantsar da sababbin shuwagabanninta, waɗanda za su jagoranci alámuran ƙungiyar tsawon shekaru uku nan gaba.
Bikin rantsuwar ya gudana ne, a Sakateriyar Ƙungiyar da ke kusa da titin Gashua, a Damaturu, babban birnin jihar.
Da ya ke jawabi, a ya yin bikin rantsuwar, shugaban Kwamitin shirya zaɓen, Ahmed Isa Abba, ya ce da dama daga cikin kujerun basu samu Abokanan hamayya ta fuskar takara ba, domin ƴan takarkaru ɗai-ɗai ne su ka miƙa takardun nuna shaáwa.
Ya kuma ƙara da sanar da cewa, har yanzu za a iya neman muƙamin Sakataren kuɗi a ƙungiyar, saboda har zuwa lokacin da aka gudanar da zaɓe kujerar bata da ɗan takara.
Za a gudanar da zaɓen kujerar ne, a wata ranar ta daban, bayan samun masu zawarcinta.