Kotu
Ba a San Maci Tuwo Ba: Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar APC, Kan Rashin Ingancin BVAS , A Zaɓen Kano
A cigaba da gabatar da hukunce-hukunce mabanbanta da ta ke yi, kan shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano, da jam’iyyar APC ke ƙalubalanta a gabanta, Kotun shari’ar zaɓen Gwamnan Kano, ta yi watsi da ƙorafin APC kan rashin sahihancin na’urar BVAS, da ma wasu kayayyakin zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi amfani da su a ya yin zaɓen Gwamnan jihar, da ya gudana a watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki.
Inda Kotun ta ce, amincewa da na’urar a hukumance abu ne da ya ke tabbatar da sahihancinta wajen daƙile maguɗi a ya yin zaɓe.
Kafin wannan hukunci na biyu kuma, Kotun ta zartar da hukunci na farko, wanda ya tabbatar da sahihancin kasancewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, a matsayin ɗan jam’iyyar NNPP.