Ba Ma Fargabar Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara – Gawuna
Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar Gwamnan jihar Kano, ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, a babban zaɓen 2023 da ya gabata, ya bayyana cewar, ko kaɗan ba sa tsoro ko fargabar hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara za ta zartar, bayan tsagin NNPP sun ɗaukaka ƙara, kan hukuncin Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Gwamnan Kano.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai, Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan Kano, ta soke nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu, tare da ayyana, Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar, bayan da ta soke wasu ƙuri’u kimanin 165,633 da ta ce an yi aringizonsu, sakamakon gaza ganin sitamfi da kwanan wata a jikinsu.
Kotun mai Alƙalai uku kuma, ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta janye takardar shaidar lashe zaɓen da ta bawa, Abba Kabir Yusuf na NNPP, tare da miƙa wata takardar shaidar samun nasarar ga, Nasiru Yusuf Gawuna, na APC.
Da ya ke bayyana godiyarsa kan wannan gagarumar nasara da su ka rabauta da ita, a ya yin ganawarsa da shafin Hausa na BBC, an jiyo Gawuna na cewa, “Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan gagarumar nasara da ya bamu a zaɓen jihar Kano, wanda Kotu ta sake tabbatarwa a yau (Laraba). Ina gode masa bisa ikonsa da ya nuna, ta hanyar zaɓarmu domin jagoranci. Ina kuma ƙara godiya ga Lauyoyinmu, da ma sauran dukkannin al’umma, bisa Addu’o’i, da goyon bayan da su ka nuna mana.
“Ko a baya ma da aka ayyana NNPP a matsayin wacce ta yi nasara, a zaɓe, na aminta da cewar Ubangiji ne ya yi zaɓinsa. Kuma doka ta bamu damar ƙalubalantar sakamakon a gaban Kotu, hakan kuma a ka yi. Wanda shi ma wannan hukunci da Kotu ta zartar ikon Ubangiji ne”.
Da aka tambaye shi ya su ke ji, kan ƙarar da NNPP da ɗan takararta su ka ce za su ɗaukaka, sai Gawuna ya ce, “Dukkannin wanda ya yi Imani da cewar babu abinda ya ke faruwà sai da izinin Allah, ba zai damu ba, ko ya ɗauki Shugabanci a matsayin ko a mutu ko a yi rai. Dukkannin abin da ya faru da mu, mun yi Imanin cewar daga Allah ne. Ko kaɗan ba ma jin wata fargaba ko damuwa, domin mun san dukkannin abin da ya faru, zaɓin Ubangiji shi ne mafi dacewa. Allah ba ya kuskure.”