Ilimi

Ba Za a Ƙara Yin Yajin Aiki A Jami’o’in Najeriya Ba – Majalissar Wakilai

Kwamitin Majalissar Wakilai kan Ilimin Jami’o’i, ya sha alwashin yin aiki tuƙuru, wajen ganin an shawo kan matsalar gudanar da Yajin Aiki, a Jami’o’in Najeriya.

Shugaban kwamitin, Abubakar Fulata, shi ne ya bayyana hakan, a ya yin tattaunawarsu da babban Sakataren hukumar kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC), da ma shuwagabannin Jami’o’in tarayya, a Abuja, ranar Talata.

Ya kuma ce, shugabancinsu ya samar da ƙarin Kwamitoci shida, baya ga guda biyun da ake da su a baya, domin yi wa matsalar Yajin Aikin duba na tsanaki.

Ya kuma ce, Kwamitin nasu na aiki ba dare ba rana, wajen tabbatar da inganta Ilimin Jami’o’i, tare da samun damar amfanuwa da shi ba tare da wani shinge ba.

A nasa jawabin, Sakataren hukumar NUC na riƙon ƙwarya, Farfesa Kiris Maiyaki, ya ce babu shakka Jami’o’in Najeriya su na fama da tarin ƙalubale.

Sai dai, ya bayyana ƙwarin guiwarsa kan cewar, tabbas za a shawo kan matsaloli da dama, muddin aka samu jajircewar majalissar tarayyar.

Ita kuwa, Farfesa Folasade Ogunsola, wacce ta yi jawabi a madadin shuwagabannin Jami’o’i, cewa ta yi muddin aka dafa, Jami’o’in Najeriya za su kai matsayin zama mafiya inganci da shuhura a nahiyar Afirka.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button