Ba Za Mu Ƙirga Ƙuri’un Dukkannin Rumfar Zaɓen Da Aka Samu Hargitsi Ba – INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta bayyana cewar za ta kai Kwamishinoninta na ƙasa guda biyu, zuwa jihar Bayelsa, tare da Kwamishinonin hukumar takwas da ke ofishin INEC na jihar, a shirye-shiryen da ta ke cigaba da yi, na gudanar da zaɓen jihar, a ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban hukumar ta INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya bayyana hakan, a Yenagoa, ya yin wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta gudanar, ya yin da yake jaddada shirin da hukumar ta yi wajen tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe.
Ya kuma yi gargaɗin cewar, hukumar ba za ta ƙirga ƙuriú a dukkannin akwatin zaɓen da aka samu tashin hankali, ya yin zaɓen Gwamnan na ranar Asabar, da zai gudana a jihar ta Bayelsa ba.
Yakubu, wanda ya samu wakilcin Kwamishiniyar INEC da ke sanya ido akan zaɓen Akwa-Ibom, Bayelsa, da Rivers, Mrs May Agbamuche-Mbu, ya ce INEC za ta áike da naúrar tantance masu zaɓe ta BIVAS zuwa dukkannin rumfunan zaɓen jihar.