Ba Za Mu Koma Gida Ba, Har Sai Gwamnatin Najeriya Ta Rage Kuɗin Lantarki – NLC da TUC
Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa (NUC da TUC), a sassan jihohin Najeriya daban-daban, tare da babban birnin tarayya Abuja, sun mamaye farfajiyoyin kamfanonin rarraba hasken lantarki, a ranar Litinin.
Membobin ƙungiyoyin, sun mamaye ofisoshin ne, da nufin tilastawa Gwamnatin Tarayya, janye ƙarin kuɗin wutar lantarkin da ta yi, ga kwastomomin da ke rukunin wutar lantarki na A.
Bayan fitar membobin ƙungiyoyin zuwa ofisoshin raba hasken lantarkin a ranar Litinin kuma, membobin sun ce ba za su koma gida ba, har sai gwamnatin tarayya ta janye ƙarin da ta yi.
Da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai, shugaban NLC na jihar Oyo, Kayode Martins, ya ce babu adalci a matakin da Gwamnati ta ɗauka na ƙara ƙaƙaba ƙarin kuɗin lantarki, a yayin da Najeriya ke cikin halin ƙaƙanikayin matsin tattalin arziƙi, gami da cire tallafin manfetur.
Shugaban ya ce, Ƴan Najeriya su na biyan kuɗin wutar lantarkin da basu sha ba.