Labarai

Ba Za Mu Shiga Zanga-Zangar NLC Ba – TUC

Ƙungiyar Ƙwadago ɓangaren masana’antu ta TUC, ta bayyana cewar, ba za ta shiga cikin zanga-zangar kwanaki biyun da NLC ta shirya, a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu ba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Festus Osifo, shi ne ya bayyana hakan, a ya yin wani taron Manema Labarai da ƙungiyar ta shirya kan halin da ƙasar nan ke ciki, ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja.

A cewarsa dai, TUC ɗin ba za ta taɓa shiga a dama da ita ta hanyar gudanar da zanga-zanga da mamaye tituna da nufin nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke ciki ba, kamar yadda NLC ta ƙudirta.

Sai dai, Osifo ɗin ya yi kira da a gaggauta kammala tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi, tare da rattaɓa hannu a kansa, domin zama doka.

TUC ɗin, ta kuma aminta da cewar, ma’aikata tare da sauran al’ummar ƙasar nan na fuskantar ƙaruwar fama da yunwa, da matsin rayuwa.

Inda ya ce, tabbatar da sahalewa mafi ƙarancin albashi zai taka gagarumar rawa wajen sauƙaƙa lamarin.

Osifo, ya kuma bayyana karya darajar Naira, da matsalolin tsaro, a matsayin manyan jiga-jigan da su ka ta’azzara lamarin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button